Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf na NNPP da kuma Nasiru Yusuf Gawuna na APC.
Saƙon kotun da ya bayyana da maryacen Laraba, na tabbatar da cewa za a yanke hukuncin ne ranar Juma'a 12 ga watan Janairu.
Shi ne matakin ƙarshe ga ɗaya daga cikin manyan shari'o'in zaɓen 2023.
Tun bayan ɗaukaka ƙara a gaban kotun ƙoli da kammala sauraron bahasin kowanne ɓangare ne, magoya bayan jam'iyyun biyu da sauran jama'ar jihar Kano ke dakon zuwa wannan rana cike da zullumi da kuma zumuɗi.
Shari'ar Kano ta kasance abin da ke jan hankali inda mutane suka zura ido domin ganin yadda za ta kaya tsakanin ɓangarori jam'iyyun biyu.
Lauyoyin ɓangarorin biyu, Barrista Abdul Adamu Fagge na APC da kuma Barrister Bashir Tundun Wuzirci na NNPP, duk sun tabbatarwa da BBC samun sanarwar kotu, game da ranar yanke hukunci.
Kowanne a cikinsu kuma na bayyana kyakkyawan fatan cewa ɓangarensa ne zai yi nasara a wannan shari'ar zaɓen Kano.
Kafin a je kotun daga-ke-sai-Allah-ya-isa, hukuncin ƙananan kotuna biyu duk sun bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP, rashin nasara a zaɓen watan Maris, kuma suka umarci hukumar zaɓe ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai Abba, sannan ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan Kano.
Hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a kan zaɓen na Kano, yana ɗaya daga mafi janyo taƙaddama da ce-ce-ku-ce a shari'o'in zaɓen 2023, saboda yadda rubutaccen hukuncin ya zo da saɓani, kafin rahotanni su ambato magatakardan kotun na cewa abin da ya faru ba saɓani ba ne, tuntuɓen alƙalami ne, kuma doka ta yi bayani a kansa.
Tuni dai ɓangarorin biyu suka koma ga Allah, inda sukan duƙufa tarukan addu'a da sallolin nafila da azumi don neman nasara a shari'ar ta kotun ƙoli.
Haka zalika, magoya bayan NNPP da APC sun yi ta jifan juna da zargin bayar da cin hanci game da wannan shari'a a ƙananan kotuna. Duk da yake babu ɓangaren da ya iya gabatar da ƙwaƙƙwarar hujja a kan zargin.
Babu abin da aka fi tattaunawa a kai tsakanin mutane a wuraren zama kamar yanayin siyasar da jiharsu ke ciki, inda wasu ke tausaya wa NNPP wasu kuma ke goyon APC.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, da kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓensa, ya ce har yanzu yana da ƙwarin gwiwar cewa Kotun Ƙolin Najeriya, za ta dawo masa da nasararsa.
Hakazalika bangaren Gawuna a ta bakin, Shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, nada kyakyawan fatan za su dara a wannan shari'a ta karshe.