Comr Musa Zangina Adam shine shugaban Kungiyar Matasan Yan Jarida reshen Jihar Kano ya yi wannan jawabin ne yayi ganawarsa da manema labarai, inda yace wannan abu da kotun koli tayi abun ayabawa fannin shari'a ne, domin samun yalwataccen zaman lafiya a Kano dama kasa baki daya.
Zangina yace duk wani matashi zaiso zaman lafiya domin idan ansami akasin haka matashi take shafa, wajen fita neman abinci ko taimakon iyaye ko karatu da dai sauransu, inda ya nemi bangaran kotuna da suyi koyi da kotun koli wajen yin hukunci akan gaskiya domin samun ingatacciyar demukradiyya har zuwa ga yaya da jikoki.
Comr Zangina ya yi kira da Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf wajen yin duk ayyukan nakwarai dama samarwa matasa ayyukanyi da sanyasu cikin duk wata tafiya da zai zamana matasa sunsan cewar gwamnati na hangen goben matasa sakamakon wataran zai zamana da matasan ake damawa.
A karshe ya kara taya Kwamishinan Watsa Labarai ta Kano Baba Halilu Dan tiye murnar samun wannan gagarumar nasara dama al'ummar Kano baki daya