Kungiyar masu shaguna a filin masallacin Idi sun mika kokensu gaban kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Usaini Gumel, inda suke neman a fara bincikar gwamnan jihar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf, bisa rushe musu shaguna da sukace yayi ba bisa ka’ida ba.
Daga cikin wadanda suke koke a kansu sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Dr Abdullahi Baffa Bichi Sai Muhammed Diggol da sauransu.
A hirarsa da manema Labarai a nan Kano, Lauyan kungiyar, Barrister Mohammed Yakasai, ya bukaci kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano da ya ‘dora daga kan hukuncin da babbar kotun tarayya, wanda ta baiyana matakin rushe shagunan a matsayin haramtacce da kuma sosa zuciya.
Yakasai ya yi zargin cewar wasu daga cikin masu shagunan da aka rushe sun rigamu gidan gaskiya a yayin da wasu suka kamu da rashin lafiya, inda ya bukaci a tabbar da adalci.
Kungiyar masu shagunan a filin Idi sunyi alkawarin gabatar da dukkanin wasu hujjoji da zasu tabbatar da zargin da suke yi.
A wani bangaren kuma, Kungiyar masu shagunan da aka rushe a filin masallacin Idi , sun baiyana cewar gwamnatin jihar kano ta biya su naira bilyan 1 daga cikin bilyan 3 data amince zata biya masu shagunan da aka rushe.