Allah shike ba da mulki ga wanda yaga dama a lokacin daya so, Allah shi yayiwa Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf nasara a hukumar zabe ta INEC aka zalunce mu a kotun karbar kararrakin zabe, muka sake tafiya kotun daukaka kararrakin zabe nan ma akai mana makamancin wannan zalunci.
Ubangiji ya nuna ikon sa a kotun karshe wacce daga ita sai Allah ya isa, a matsayina na mataimakiyar shugaban gidan talabijin na abubakar rimi ina mai kara taya Zababben Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf murnar samun wannan nasara Allah ya cigaba da shiga lamuransa yayi riko da hannayensa.
Godiya ta musamman ga alkalan kotun koli masu daraja, dama al'ummar da suka ringayiwa Gwamnatin addu'oi babu dare babu rana, Godiya ga ilahirin yan kwankwasiyya bazan gusheba sai na mika godiya ta musamman ga Jagoran mu na darikar kwankwasiyya na duniya Engr Dr Rabi'u Musa Kwankwaso Allah ya biya masa bukatunsa.