Saraki ya taya Gwamnonin Zamfara, Bauchi, Plateau da Akwa Ibom murnar samun nasara a kotun ƙoli
Tsohon shugaban majalisar dattawan Nigeria Dr. Abubakar Bukola Saraki ya taya gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom da Bala Muhammad na Bauchi da Dauda Lawal Dare na Zamfara da kuma Caleb Muftwang na Plateau murnar nasarar da suka samu a kotun ƙoli a shari'un gwamna da aka yanke a yau.
Saraki, wanda tsohon gwamnan jihar Kwara ne ya bayyana cewar wannan nasara da gwamnonin suka samu nasara ce ga dimokuraɗiyyar Nigeria.
"Ina miƙa saƙon taya murna ta ga Umo Eno da Bala Mohammed da Dauda Lawal da kuma Caleb Muftwang sakamakon nasarar da suka samu a kan zaɓukansu a kotun ƙoli."
"Tabbatar musu da kujerunsu da kotu tayi ya nuna cewa ana bin tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar mu."
Saraki ya ce yana mai tabbatar musu da goyon bayansa wajen ci gaba da ayyukan alheri ga al'umominsu.
A yau ne dai kotun ƙoli ta yanke hukuncin ƙarar da aka shigar a gabanta na zuɓukan gwamnonin da aka yi a shekarar da ta gabata.