Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamna Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf murnar samun karin shekaru a duniya.
Tinubu ya amince da tsayuwar daka a cikin siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta hanyar siyasa.
Ta cikin sanarwar da Chief Ajuri Ngelale, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman, Yace Shugaba Tinubu ya yi wa Gwamnan fatan samun nasarar gudanar da ayyukan sa.
Shugaban ya kuma yi addu’ar Allah ya kara masa shekaru masu yawa cikin koshin lafiya.