Wata Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ƙarƙashin mai shari’a Garba Hamza Malafa tayi amai ta lashe bayan data janye umarnin kamo wani jami’in hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa wato Kwastam inda tayi iƙirarin bijirewa umarnin ta na ƙin bayyana a gabanta bayan data nemi ganin shi, kuma wanda ake ƙarar bai turo da wakilci ba kamar yadda tayi iƙirari.....
Ga Yadda al'amarin ya faru a baya-bayan nan shine......👇👇👇
Yace wanda ya shigar da kara, Aliyu ya garzaya kotu yana roƙon kotu data bada umarnin damko Yusuf bisa zargin cewa wanda ake kara yayi barazanar mallakar kadarorinsa mai lamba 1,136 C dake Kawaji layout, a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.
Ya kuma yi zargin cewa Yusuf Ismail Mai Biscuit da aka manna masa takardar gayyata da jan fenti a bangon gidansa, ya umarce shi daya rabu da kadarorin da gama mallakar su ba duk da cewa ya mallaki kadarar ne bisa ka’ida daga hannun ainihin mai gidan.
Da aka gabatar da karar a ranar Alhamis, lauyan mai kara, Barista Idris Saleh Bello, ya shaidawa kotun cewa wanda ake kara baya gaban kotu kuma bai turo da wakilci ba.
Ya kuma roki kotu da tayi amfani da karfin da take dashi wajen zartar da hukuncin kamu wanda ake kara.
Ya kuma nemi da tasa a kama shi, bisa tanadin sashe na 352 na ACJL 2019.
Barista Bello ya bayar da hujjar cewa mai gabatar da kara na kotun ya mikawa wanda ake kara sammacin kotu, inda ya bukace shi daya halarci kotun a ranar 4 ga watan Janairu.
“Muna sane da cewa kowa yana bin doka da oda, yanzu karfe 10 na safe kuma an sanar da wanda ake kara bisa ga takardar sammacin cewa kotu zata fara zama da karfe 9 na safe, rashin halartar kotun a yau ba tare da wani dalili ba shine raini, a saboda haka kotu wanda ya zama laifi".
A sakamakon haka, Kotun tayi tambaya daga mai bayar da belin wanda ya tabbatar da cewa ya yiwa wanda ake tuhuma takardar sammaci hannu da hannu. Nan take ya nunawa kotu shaidar cewa ya bayar
Alkalin kotun, Garba Hamza Malafa ya umarci ‘yan sandan Najeriya da su kamo wanda ake kara kamar yadda aka buƙata.
"Duk da cewa wanda ake kara baya gaban kotu bai kuma turo da wakilci ba, ba tare da wani dalili ba, amma mai bayar da belin ya tabbatar wa kotu cewa ya mika sammacin ga wanda ake kara, wannan karar kai tsaye korafi ne daga lauyan wanda ake kara, don haka yana da matukar muhimmanci wanda ake kara ya halarta kotu"
A don hakaMai Shari’a Garba Malafa yace
Kotun ta tsayar da ranar 8 ga watan Janairu.
....................
.
A saboda haka bayan bincike da fahimtar kuskuren da aka tafka a waccan takarda kotun dai ta janye wancan nema tare da saka rana domin cigaba da sauraron wannan shari’a.