Mazauna garin dai sun ce 'yan bindigar karkashin jagorancin gawurtaccen dan bindigar nan a yankin, Damuna sun afka musu ne saboda sun gaza biyan harajin naira miliyan ashirin da dan bindigar ya dora musu.
Jihar Zamfara na fama da hare-haren 'yan bindiga da sace tare da garkuwa da al'umma domin kudin fansa, inda da wuya rana ta fito ta fadi ba a ji irin wadannan munanan labarin ba.
Wata uwa da aka kashe wa da ta ce "muna zaune muna gudanar da al'amuranmu kawai sai muka ji harbi. Sai muka kwasa da gudu, a inda 'yan bindigar suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi. Ina fatan za a sako min 'ya'yana".
Shi ma wani wanda mazaunin garin ne ya shaida wa BBC cewa " yanzu haka akwai mata fiye da 50 da ke hannunsu a cikin daji".
To sai dai gwamnatin jihar a ta bakin mai magana da yawun gwamnati, Sulaiman Bala Idris, ta ce ana samun sauyi sabanin yadda jihar ta Zamfara take a baya, "ina mamakin yadda jama'a ba sa fadar irin nasarorin da gwamnatin nan ke samu. Ko a shekaran jiya sai da aka kashe gagga-gaggan 'yan bindiga".
A watan Nuwamban badi dai wasu maharan sun yi garkuwa da kimanin mutum dari da suka hada da mata da yara daga garuruwan a matsayin mayar da martini sanadiyyar wani hari ta sama da sojoji suka kai a maboyarsu.