Wani mai suna Nura Balarabe mazaunin Kwanar Mahuta dake yankin Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano ne ya shigar da karar wani matashi mai suna Ukasha Muhammad, Mazaunin Garin Langel ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa bisa zargin yayiwa kanwar sa mai suna Amina Bala ciki.
Ya kuma hada baki da wani likitan bogi mai suna Chidera Ugwu wanda ke zaune a garin Lambun bankin dake Dawakin Tofar, inda wannan likitan bogin yayi mata allura hadi da bata magunguna da niyyar zubar da cikin datake dauke da shi, wanda a karshe dai tace ga garinku nan.
Jami'in Hulda da Jama'a na Rundunar 'Yansandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa yace, jami'ansu sun sami nasarar cafke dukkanin masu hannu a ciki wanda kuma duk sun amsa laifin da ake zarginsu dashi, Kiyawa yace cikin binciken da rundunar yansanda suka gudanar akan likitan bogin ya tabbatar da cewar yadade yana wannan sana'ar ta zubda cikin mata wanda hakan ke haddasa wa matan matsaloli masu tarin yawa.