Yanzu-Yanzu wani matashi me suna Nuraddeen ya rataye kansa a ƙaramar hukumar Gwalen jihar kano.
Wakiliyar jaridar Raihana sashen hausa Maryam Shehu Sulaiman ta rawaito mana cewa matashin ya rataye kansa ne a wata makaranta mai suna Prestige wanda ba'a gano ya rataye kan nasa ba sai bayan kwana biyo da afkuwar al'amarin.
Bayan da aka gano shi ne aka sanar da jami'ai inda nan take suka je don yin binciken musabbabin faruwar al'amarin tare da aike da gawar zuwa asibiti.
Wakiliyar tamu ta samu damar zantawa da Mahaifiyar matashin inda ta bayyana mana cewa yana da larurar ƙwaƙwalwa, sannan ya samu damar yin aure a baya amma auren ya rabu, ta kuma ƙara da cewa tun bayan da auren nasa ya rabu ne ya abun ya ƙara girmama saboda damuwar rashin matarsa.