Alfijir labarai ta rawaito hukumar kare hakkin masu sayan kaya ta kasa (Federal Consumer Protection Council), ce ta dauki wannan mataki da safiyar juma’a.
Rahotanni sun ce, kantin na Sahad Store da ke Abuja, yana karbar kudin kayan da abokan huldarsa suka saya da ya sha banbam da abin da aka rubuta a matsayin kudin kayan da ke ajiye a kanta; ma’ana idan aka rubuta Naira 100 a jikin kaya, in kaje biyan kudi sai ace Naira 200 ne.
A jiya alhamis ne shugaban kasa Bola Ahmed TINUBU ya shaidawa gwamnonin Nigeria cewa, ‘yan-sanda, jami an hukumar tsaro ta DSS da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki na gwamnatin tarayya, za su fara bi lungu da sako na kasar nan domin zakulo inda ‘yan kasuwa suka boye kayayyakin abinci domin jira yayi tsada.