Hakan na zuwa ne bayan matakin mayar da wasu ma'aikatan babban bankin Najeriya, CBN da sauya matsugunin hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya - FAAN zuwa Legas.
Wasu ma'aikatan NUPRC sun bayyana matukar damuwa kan wannan yunkurin saboda a cewarsu zai shafi yadda suke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Hukumar NUPRC ita ce ke lura da mai da iskar gas domin tabbatar da bin ƙa'idoji da dokokin da suka dace da kuma lura da wasu dokoki da suka shafi fita da shigowa da albarkatun mai cikin Najeriya.
NUPRC da a baya ake kira DPR a ƙarƙashin ma'aikatar albarkatun man fetur ta Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito tuni aka aika wa sassan hukumar na NUPRC wata wasika da ke nuna sabon matakin da ake kokarin dauka na kai wadansu ma'aikata zuwa Legas.
A yanzu haka dai ana gina wani sabon ofishin hukumar NUPRC mai hawa 10 a Abuja wanda zai kunshi dubban ma'aikata kuma ana sa ran a wannan shekarar za a kaddamar da shi.