Duk wanda yasan ya boye kayan abinci ya fito dashi kafin muzo -Inji Muhyi Magaji Rimin Gado.
Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da Rashawa ta jihar Kano Barrista Muhyi Magaji Rimin Gado zai fara Kai ziyara runbunan ajiyar Kayan Abinci a Kano Dan fito da abincin da aka boye a sayarwa da jama'a.
Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yace Haramun ne Kuma karya dokar kasa ne boye abinci Lokacin da ake tsanananin wahalar abinci a kasa .
Za'a fara Kai samamen guraren da ake zargi an boye kayan Abinci ne kafin watan Azumin Ramadan.
Muhyi Magaji Rimin Gado yace wajen da zasu fara Dira shine Kasuwar Dawanau inda yace duk Wanda aka kama ya boye abinci za'a fito da abincin a kaishi kasuwa, wanda hakan Zai taimaka wajen sauko da farashin kayan Abinci.