Tsarin IPPIS tsari ne da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta daÉ—e tana amfani da shi wajen biyan ma’aikatanta, inda ake É—aukar bayansu ciki har da zanen yatsun hannu, da nufin rage rashin gaskiya da wasu ke yi na yin aiki a hukumomin gwamnati daban-daban suna karÉ“ar albashi fiye da É—aya.
sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Talata, Gwamna Abba Gida-Gida kamar yadda aka fi saninsa, ya ce ya bijiro da wannan tsari ne don tabbatar da gaskiya da rashin rufa-rufa da Æ™eÆ™e-da-Æ™eÆ™e wajen tafiyar da al’amuran gwamnati.
Gwamnan ya ƙaddamar da tsarin da aka bai wa suna Kano Integrated Personal and Payroll Information System (KIPPIS) ne a wajen taron Majalisar Zartarwa karo na 12 da aka yi a fadar gwamnatin jihar.
Abba Gida-Gida wanda ya zamo mutum na farko da aka dauki bayanansa aka dora a kan manhajar tsarin, ya ce za a yi amfani da shi ne a duka matakin jiha da na Æ™ananan hukumomi “don bin tsarin sha’anin kuÉ—i da duniya ke kai a yanzu.”
Gwamnan ya nei mambobin kwamitin Æ™addamar da tsarin KIPPIS da su tabbatar da cewa sun É—auki bayanan dukkan ma’aikatan gwamnati da Æ´an fanshi da masu riÆ™e da muÆ™aman siyasa don samun nasarar tsari a faÉ—in jihar.
Kazalika Babban Akawun jihar Alhaji Abdulkadir Abdussalam, ya ce za a tabatar da cewa ba a samun matsaloli ba a wajen bin tsarin KIPPIS ta kowane fanni da suka haÉ—a da rage kuÉ—aÉ—en mutane.