Hukumar tace fina finai da dab'i ta jihar Kano zata fara rarraba jami'anta mata na sirri a Gidajen biki domin yaƙi da masu sai da magungunan gargajiya masu dauke da hotunan batsa.
Hakan ya biyo bayan wata ganawa da shugaban hukumar Alh Abba El-mustapha yayi a sifiyar wannan rana ta Alhamis da manema labarai,
Inda yace hakan baya rasa nasaba da yadda hukumar tasu ta dukufa akan kasuwanni a baya, amma duba da wasu bincike da hukumar ta gudanar na sirri ya sanya su daukar wannan mataki.
Haka Kuma yakara da cewar hukumar tasu zata kara daukar mataki da dukkanin wasu masu sana'ar buga takardun da suka danganci hotunan batsa.
Daga karshe shugaban hukumar ya godewa sauran jami'an tsaro musamman ma wadan da suke kula da bangaren sufuri.