Ƙudurin wanda ke neman a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, ya samu goyon bayan ‘yan majalisa akalla 90 a cikin 360 kuma idan ya tabbata hakan zai sa a koma tsarin Firaminista kamar yadda aka yi zamanin jamhuriya ta daya.
‘Yan majalisar da suka goyi bayan Æ™udurin sun amince cewa tsarin shugaban Æ™asa da Najeriya ke kai ya gaza.
Sun ce tsari ne da ake da yawan jami’an gwamnati wanda dalilinsu kuÉ—aÉ—e masu yawa da ya kamata a yi wa al’umma aiki da su ke tafiya a wata hanyar ta daban.
Sun ce suna son a koma kan tsarin da aka bai wa Najeriya ‘yanci a kai, wanda muradun al’umma ne babban abin da shugabanni suka sanya a gaba.
Tsari ne wanda ake fito da masu tsara dokoki da masu zartarwa daga cikin zaɓabbun da mutane suka zaɓa da kansu a lokutan zaɓe.
Abdussamad Dasuƙi daga jihar Sokoto wanda ke jagorantar wannan yunkuri, ya ce "a shekaru shida da aka yi ana tafiyar da Najeriya kan tsarin Firaiminista, ƙasar ta kasance kan turba mai kyau. "
"Wannan tsarin shi muka iske tun lokacin su Sardauna, kuma ya yi aiki amma tun da aka bar shi ba mu sake gane kan mu ba, a matsayinmu na Æ´an Najeriya, shi ya sa muka ce gwara mu koma ma abin da ya yi mana aiki."
"Tsarin firaminista muke so a koma wanda za a riƙa zaɓar shugaban ƙasa da firaminista da ministocinsu daga cikin ƴan majalisa," in ji Abdussamad Dasuƙi
Ɗan majalisar ya ce yin hakan zai taimaka wajen rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen harkar gwamnati, "Idan aka lura za a ga ƙudaden da ya kamata mu kai a ɓangaren ilimi da lafiya da sauran ɓangarori su ne ake hidimar gwamnati."
Abdussamad Dasuƙi ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ba su hadin kai wajen cimma ƙudurinsu.
Shi ma a nasa bangaren Barista Muhammad Bello Shehu Fagge ɗan majalisa daga jihar Kano ya ce wasu daga cikin komabayan da ake fuskanta a tsarin gudanar da gwamnati na shugaban ƙasa, akwai yawan kashe kudi, da ƙayyade ayyukan ci gaba.
"A yanzu mun kai mu 90 da muka amince da ƙudurin, kuma duk 'yan majalisa ne da suka fito daga dukkan sassan Najeriya, kuma babban abin da muke so mu cimma wa shi ne a rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen harkokin gwamnati, " in ji Barista Bello Shehu.
‘Yan Majalisar dai na son a fara amfani da tsarin gwamnati na firaminista nan da 2031, inda za a maye gurbin zaÉ“aÉ“É“en shugaban Æ™asa da Firaminista.
Tsarin dai zai zama ba a kashe kuɗin gwamnati wajen gudanarwa, sannan kuma zai saukaka jan ƙafar da ake yi wajen tsarawa da aiwatar da dokoki a hukumance.
Tsarin firaminista
Ƴan majalisar na Najeriya na son ƙasar ta koma tsari ne irin na Birtaniya inda firaminista zai kasance shugaban gwamnati.
Najeriya ta taɓa amfani da tsarin firaminista kafin samun ƴancin kai da kuma zamanin jamhuriyya ta farko. Sai dai juyin mulkin 15 ga watan Janairun 1966 a kawar da tsarin.
Sojoji suka hamɓarar da gwamnatin ta farar hula sannan suka ci gaba da mulki har zuwa 1979, amma kuma kuma a zamanin na jamhuriyya ta biyu aka yi tsarin shugaban kasa mai cikakken iko
A tsarin Firaminista, É“angaren zartarwa zai samu halacci ne da iko daga majalisa.
Kuma shugaban gwamnati wanda shi ne firaminista mamba ne a majalisa. Kuma wannan tsarin na ƙarfafa dangantaka tsakanin ɓangaren zartarwa da kuma majalisa.
Tsarin yana sauƙaka ayyuka da yanke shawara mai inganci da kuma saurin aiwatar da manufofin gwamnati
Sai dai masana na ganin tsarin firaminista yana da ƙalubale musamman yadda wasu tsiraru ne za su zaɓi shugaban gwamnati saɓanin al'ummar ƙasa, wanda mafi yawanci ke sa sojoji ƙwatar mulki