Alfijir labarai ta rawaito hukumar Hisbah ta cafke ta tare da gurfanar da ita a gaban kotun, bayan ta karbi korafe-korafen mazauna unguwar Tishama a karamar hukumar Nasarawa dake Kano.
Bayan gurfanar da ita a gaban kotun an karonta mata kunshin zargin, inda ta musanta dukkan tuhumar da ake yi mata.
Lauyan dake kare wadda ake tuhumar Barista Aliyu Umar ya roki kotun ta bayar da belin ta, dogaro sashi 35 da 36 na dokokin kasa da kuma sashi na 168, 172 da 173 na kundin SPCL.
Lauyan gwamnatin jahar Kano da ya wakilci kwamishinan shari’a na jahar Kano, Barista Aminu Umar bai yi suka akan rokon wadda ake tuhumar ba.
‘’ Ba mu da suka akan wannan roko domin bayar da beli hurimin kotu ne’’ lauyan Gwamnatin Kano’’.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wadda ake zargin a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 22 ga watan fabarairun 2024.