Ziyarar bazata zuwa GGSS Coexist Azare, Gabasawa
Mai girma kwamishinan ilimin jahar Kano, Hon Umar Haruna Doguwa yakai ziyarar bazata zuwa makarantar GGSS Coexist (cikawa), Azare, Gabasawa a wannan safiyar wannan rana ta litinin 05/01/2024.
Da misalin Karfe 8:35na safiya, mai girma kwamishina ya kai ziyara wannan makaranta amma malami guda 1 tak ya samu a makarantar sannan da dalibai 11 kurum.
A firamaren makarantar malamai da daliban makarantar dukka basu zo ba.
Inda Kwamishinan ya bayyana rashin jindadinsa, kuma nan take ya karbi lambar lambar wayar hedmastan makarantar ya kirashi.