Bayan Gaisuwa tare da fatan kuna lafiya muna masu alfahari da ku bisa gudun mawar da kuke bayar wa wajen gina dokoki masu amfani ga alumar jahar kano da samar da cigaban alumar jahar Kano Kamar yadda mai girma zababban gwamnar jahar Kano His Excellency Engr. Abba Kabir Yusuf yake yi shima a koda yaushe Allah ya ci da jahar mu gaba baki daya ya karamana zaman lafiya a kasa baki daya.
Baya da haka makasudin rubuta wannan wasika gareku shine mun samu labarin wata kungiya guda daga cikin kungiyoyin jahar Kano wadda take da suna kamar haka (Yan Dangwalen Jahar Kano) ta rubuta takarda zuwa ga zauran wannan majalissa mai girma ranar 5th February 2024 da adireshi zuwa ga shugaban wannan majalissa kan rokan a rusa masarautu a dawo da ita guda daya. Bisa girmamawa ga wannan zaure muna masu barranta kanmu da wannan kuduri nasu muna kuma san a barmana masarautunmu guda biyar domin tin tarihin jahar Kano Kafin zuwan turawan mulkin mallaka muna da tsari na wadannan masarautu masu girma da daukaka dan haka tun da tarihi ya dawo da su muna da bakatar su a wannan zamani domin yawan alumma da muke da su a cikin wannan jihar ta mu wanda masarautun suna taimakawa wajen isar da cigaban da gwamnati take kawowa domin gina alumma, haka zalika masarautun da suke da nisa da cikin birnin Kano sun kara
Sannan muna masu kira ga kungiyoyi jihar Kano musamman na matasa da su maida hankali wajen taimakawa gwamnati domin zakulo ayyukan cigaban alumma, sannan su kaurace wa yin wasu kalamai wadanda zasu kawo hargitsi da kuma cece kuce hadi da tashin hankalin alummar jahar Kano. Domin ita kungiya ana gina tane domin gina alumma muna wa kungiyoyin kano fatan alkhairi da nasarorin gina alumma baki daya.
Daga karshe muna masu kira da alumma da muzama masu hakuri bisa yanayin tsadar rayuwa da ake a yanzu da bawa gwamnati goyan baya da masarautun mu domin cigaban jahar mu ta Kano. Muna masu godiya ga jamian tsaron jihar Kano gaba daya bisa gudun mawar da suke bayar wa a koda yaushe domin zaman lifiyar alummar jahar Kano, Allah ubanagiji ya kara dafa musu.
Wassalamu Alaikum Warahmatullah.