Mai martaba sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya tallafawa wani mai bukata ta musamman, kamar yadda guda daga cikin hadiman sarkin Alh. Zahraddeen Muhammad Yakasai ya wallafa.
Malam Anas na daga Cikin Masu Buƙata ta Musamman da Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya Share masa Hawaye, Inda ya Gwangwaje shi da Sabon keken hawa domin cigaba da gudanar da Al'amuran Rayuwarsa cikin Sauki, Lamar kowanne mutum Mai koshin Lafiyar Kafa.
Malam Anas Haƙiƙa ya nuna Farin Cikinsa da Murnarsa tare da Ƙara godewa Mai Martaba Sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero duk dai a Sanadiyyar siya masa sabon keken hawa.
Daga karshe mai martaba sarkin yayi kira ga mawadata wajen tallafawa nakasa dasu musamman a irin wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa