Kiran na zuwa ne a ranar rantsar da sabbin shugabannin kungiyar daya gudana a ranar laraba, ta bakin mataimakiyar shugaban talabijin na Abubakar Rimi.
Hajiya Hauwa Isah Ibrahim wacce ta sami halattar bikin rantsuwar tace yin aiki tukura da jajircewa da gaskiya da tsoron Allah sune hanyoyin da zasu samar da cigaba acikin kowacce al'umma,
Bayan karbar rantsuwa ga shugabannin kungiyar ta (Rattawu) na gidan talabijin na Abubakar Rimi, ta jagoranci bawa shugabannin certificate na shaidar kama aiki, Madi'u Adamu shine wanda aka tabbatar a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar tare da sauran shugabanci wanda gidan talabijin din ya zaba domin su zama jakadunsa a kungiyar ta (Rattawu)
Daga karshe Hajiya Hauwa Isah Ibrahim tayi musu fatan alkhairi wajen gudanar da ayyukansu.