Wani shaida da EFCC ta kira, mai suna Bamaiyi Meriga ya tabbatar wa kotu ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Hamza Muazu cewa binciken kimiyya da aka yi wa takardun - da aka sanya hannu a kansu don cire kudin - ya nuna cewa sa hannu da hatimi da aka yi amfani da su wajen cire kudin ba daidai suke da na ainihi ba.
Ya kuma tabbatar da cewa sa hannun ba na tsohon shugaban najeriya Muhammadu Buhari ba ne, kuma ba na tsohon sakataren gamnatin tarayya, Boss Mustapha ba ne.
An gabatar wa alƙalin da ke jagorantar shari'ar takardun biyu, masu ɗauke da umarnin shugaban ƙasa a matsayin shaida, sannan kuma ya amince da su.
Bayan da lauyoyin Emefiele suka nuna ƙorafinsu game da takardun, shaidar ya ce shi ba ma'aikacin EFCC ba ne kuma ba hukumar ce ke biyan sa ba.
Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya nuna rashin amincewarsa da shaidar, yana mai cewa shaidar ya yaudari kotun ne don kauce wa tambayoyin da za a yi masa.
To sai dai lauyan masu shigar da ƙara, Rotimi Oyedepo, bai ji dadin kalaman lauyan wanda ake ƙarar ba.
An dai É—age shari'ar zuwa ranar 1 ga watan Maris domin ci gaba da shari'ar.
Emefiele na fuskantar shari'a a kotun kan laifuka 20 da suka ƙunshi zargin cin hanci da haɗin baki da cin amana da amfani da sa hannun bogi wajen cire kudi har dala 6,230,000.
Ana zargin sa da sa hannun bogi na tsohon sakataren gwamnatin ƙasar Boss Mustapha wajen ciye kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba.