Horaswar ta gudana ne a babbar helkwatar su a nan kano, Inda babban kwamandan Alh. Ubale Barau Badawa yaja hankalin su Na ganin sun Maida hankali sun saurari abubuwan da Ake Koya musu Na doka da yadda zasu kiyaye ta.
Taron ya Samu halartar shugaban sashen bincike na musamman Na kasa daMukhtar Dahiru Ungogo yace wannan bita an shirya ta ne don bayyana Yan Vigilante hanyoyin da zasu bi don taimakawa jami'an tsaro a kasa baki data.
Shima manajan kamfanin tsaro me Zaman Kansa wato (international security organisation) Hafizu Shehu Ringim yayi ƙarin haske dangane da wannan bita ta musamman da aka shirya Inda ya bayyana cewa sunyi tunanin basu gudunmawa ne Duba da ganin yadda suke gudanar day aiki ba tare da cewa ana biyan su wani abu ba hakan ne yasa sukayi tunanin basu tasu gudunmawar domin karfafa musu gwiwa.