Anyi kira da mawadata wajen kara kaimi domin tallafawa mabuka musamman cikin wannan wata na Ramadan.
Kiran na zuwa ne ta hannun Mataimakiyar Gidan Talabijin na Abubakar Rimi, Hajiya Hauwa Isah Ibrahim,
Hajiya Hauwa tace dole a yabawa wasu daga cikin mawadata da suke kokarin tallafawa mabukata, musamman a jahar Kano.
Tace kamata yayi a ringa rige-rige wajen ayyukan alkhairi, musamman da taimakon kayan masarufi, domin shine abinda talaka yake tsananin bukata a halin yanzu,
Hajiya Hauwa ta kara da cewar lallai duk bawan dayakeson Allah ya yalwata dukiyarsa a gidan duniya da kiyama to tabbas yayi amfani da damar da Allah ya bashi domin cin moriya mara adadi.
Ta kuma yabawa Gwamnan Kano Alh. Abba Kabiru Yusuf da kiran dayayiwa shugaban kasa Tinubu na bude iyakokin kasar nan, inda tace tabbas Gwamnan ya taka muhimmiyar rawa sakamakon shugaban kasa baiyi wata-wata ba har yabada umarnin bude iyakokin kasar Najeriya da kasar Nijer.
Idan tace Gwamnan Abba K Yusuf irinsu ake bukata a wannan lokaci, kuma tana da yakini shugana Tinibu zai bude ragowar iyakokin Najeriya domin tsamo talaka daga halin dayake ciki a halin yanzu.
A karshe ta mika sakon barka da shigowar watan Ramadan da maigirma Gwamnan Kano da mataimakinsa da al'ummar jihar Kano.