Wata majiyar sirri daga gidan gwamnatin jihar Kano ta bayyanawa Jaridar Raihana mana cewa gwamnan na wannan shirin tun a farkon azumi wanda har shirye-shiryen yayi nisa duk domin samar da kyakkyawar mu'amula tsakanin tsaffin gwamnatocin gwamnati da sauka gabata dama me ci a yanzu. Majiyar tace ciki har da gwamnonin soje.
Tun shigowar watan azumin Ramadan gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf yake ta ƙoƙarin haɗa shan ruwa da ma'aikata a fadar sa dake gidan gwamnatin jihar Kano, inda ya sha ruwa da kwamishinonin sa da sauran ma'aikatu duk domin ƙarawa juna fahimta da kuma ganawa ta musamman.
tsaffin gwamnonin da mataimakan su da ake sa ran halartar su, sun haɗar da:
Dr. Abdullahi Umar GANDUJE da Mataimakin sa
Prof. Hafizu da
Dr. Nasiru Yusuf Gawuna
Sen. Ibrahim Shekarau da mataimakin sa
Abdullahi T Gwarzo
Gwamnan ya gana da manyan malamai wanda a jawabinsa yake nuna alhinin rashin guda cikin su bayan ya bayyana farin cikinsa da ganin wasu, inda yace zai so ace sun haɗu da wancan malami da ya cigita.
Wata majiyar sirri daga gidan gwamnatin jihar Kano ta bayyanawa Jaridar Raihana mana cewa gwamnan na wannan shirin tun a farkon azumi wanda har shirye-shiryen yayi nisa.