Wannan ne kashi na biyu kuma na karshe---Gwamnatin Kano
Daga Rabiu Sanusi
Gwamnatin jihar Kano tace zata biyama kimanin dalibai dubu ashirin da hudu da dari shidda da hamsin da daya(24,651) kudin makaranta daga makarantun gaba da sakandire guda 12 dake fadin kasar nan.
Bayanin hakan na zuwa ne daga bakin shugaban hukumar bada tallafin ilimin gaba da sakandire na jihar Kano Alah, Kabir Haruna Getso a wata zantawa da yayi da manema labarai a ranar litinin din nan.
Kabir Getso yace kasancewar mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano na da san Al'umma su samu ilimi kuma duba da irin yanayin da ake ciki na kunchin rayuwa yasa yayi tunanin biyama wadannan dalibai da suka fito daga Jami'o'i da kwalejoji daban-daban.
Shugaban ya kuma tabbatar ma da al'umma cewa a halin yanzu jami'an hukumar sa suna kan hanyar zuwa jihohin da Daliban suke karatu dan tantance su tare da turowa ofishin hukumar tare da hada dukkan bayanan da yakamata dan tura ma mai girma Gwamna kamar yadda ya bukata.
"Wannan zuwa da jami'an mu zasuyi zai bamu damar gane su wanene yan asalin jihar Kano, sannan musan kowane dalibi tare da abinda yake karanta."
"Kuma ina ganin gwamnati tace wannan ne karo na biyu bayan biyan kudin makarantar daliban jami'ar Bayero da tayi kwanan baya, dan haka kada iyayen yara su saki jiki dan ganin gwamnati ta biya suce bazasu biyama yaran su kudin makaranta ba.
Gwamnatim dai tace kasancewar abubuwan da yawa a halin yanzu,daga wannan karon baza su biyama wa su dalibai kudin makarantar ba, sai dai akwai shirin da Gwamnatin ke yi dan shiga lungu da sako na fadin Qasar nan na lalubo dukkan Dalibai Yan asalin jihar Kano tare da sa su cikin tsarin biyan su na scholerahip kamar yadda ta saba.
" wannan aikin tantancewa zai dauki jami'an hukumar mu kwanaki 3 ne kacal watau daga gobe Talata har zuwa ranar Alhamis sannan a kammala, dan haka dukkan dalibin dake karatu a wadannan makaratu guda 12 idan baya makaranta yayi kokarin komawa.
Shugaban hukumar yace makarantun da za'a tantance daliban sun hadar da Jami'ar Gwamnatin tarayya dake Dutsin-ma da Jami'ar Marigayi Ummaru Musa da su ke a Katsina sai kwalejin ilimi dake Kano da kwalejin koyar da aikin noma dake Hotoro Karamar Hukumar Taraunin jihar Kano.
Sauran sun hadar da Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau, Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi da Jami'ar Sule Lamido Jihar Jigawa da kuma Jami'ar Ahmadu Bello dake Zarian jihar Kaduna tare da Jami'ar Tarayya dake Gombe da Jami'ar Usman Dan fodio dake Sokoto sai kuma Jami'ar jihar Borno.