Akintunde Sawyer, Babban Sakatare na Asusun Bada Lamuni na Ilimi na Najeriya (NELFUND), ya bayyana hakan a wata hira da yayi da ARISE NEWS, wadda Businessday ta sanyawa ido.
An sake jingine lamunin da aka tsara zai fara a ranar Alhamis, saboda akwai wasu gyare-gyare da ake yi a Kansas kafin kaddamarwar a cewar Sawyer.
"Abin takaici, yadda wasu masu hannun da shuni sukai burus da al'amarin ba tare da sa hannun da Kuma Bada shawarwarin da sukai dace yayin gabatar da wannan tsarin Bada lamuni na daliban najeriya ba"
Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin dokar ne a watan Yunin 2023, don kafa Asusun Lamuni na Dalibai (SLF) don bayar da lamuni marar ruwa ga ‘yan Najeriya masu neman ilimi.
Shugaba Tinubu ya sanar da fara shirin ne a watan Janairun 2024, bayan da gwamnatinsa ta gaza cika wa’adin watan Oktoban bara. Gwamnatin tarayya ta dage kaddamar da shirin bayar da lamuni na daliban Najeriya ne saboda duba don yin wasu gyare-gyare Wanda zai saukakawa yan najeriya yayin karbar wannan bashi