Hassan Youth yayi wannan yabawar a lokacin zantawarsa da wakilinmu Jameel Lawan Yakasai, inda yace su a yankinsu laya tayi kyan rufi, bisa sahalewar Gwamnan Kano na zabo musu Dr Kabiru Hussain Zawachiki a matsayin Kantoman karamar hukumar,
Haka kuma yace tundaga zaben Gwamnan Kano na jam'iyyar su ta NNPP wato dai Alh. Abba K Yusuf zuwa, sanata rufa'i sani hanga da dan kawu a matsayin dan majalisar tarayya, dama mudasir zawachiki, dama sabon kantoman nasu Hon Dr Kabiru Hussain Zawachiki babu bara gurbi a cikin su.
A don haka yace bazai gusheba sai yayi godiya ga Allah (sw) a bisa addu'oin su daya karba na azurtasu da shugabani na gari.