Ku yi hakuri bisa rashin wutar lantarki da ake fama da shi, Gwamnati ta roki ƴan Najeriya
Ministan ma'aikatar samar da hasken wutar lantarki a Najeriya, Bayo Adelabu ya ce yana cike da damuwa kan yadda ɓangaren samar da wuta ke ci gaba da taɓarɓarewa a faɗin ƙasar.
Ministan na lantarki ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya nuna ɓacin ransa kan raguwar wutar lantarki da ake samu duk da irin kokari da ake yi a ɓangaren.
“Dangane da haka ne na gayyaci shugabannin kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) da kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC), da kuma Babban Darektan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN), zuwa wani muhimmin taro,” in ji ministan.
Ya ce makasudin kiran taron shi ne tattaunawa kan taɓarɓarewar wutar lantarki a yankunansu da kuma ganin an samar da mafita mai ɗorewa kan hakan.
Mista Adelabu ya ce ma’aikatarsa ta yi ta matsa wa masu samar da wutar lantarki da su ƙara kokari a ayyukansu, abin da ya sa ma har aka ƙara karfin megawat na wuta zuwa 4000.
Ya ce duk da irin ci gaba da aka samu, wasu kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun kasa rarraba wutar lantarki da TCN ke bayarwa yadda ya kamata, yayin da ake ƙara samun masu satar da kayayyakin wutar lantarki musamman a yankuna kamar Abuja, Benin, Fatakwal, da kuma Ibadan.
Ya ce ba za su lamunci rashin samar da wuta ba daga kamfanonin da alhakin haka ya rataya a wuyansu, kuma za a ɗauki mataki mai tsanani a kansu, ciki har da soke lasisi.
Ministan ya ce ana ci gaba da tsare-tsare na ganin an warware basussukan da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki da iskar gas, wanda hakan zai rage wahalhalun da ake fama da su.
Don haka, ya buƙaci jama’a da su ƙara hakuri yayin da ake aiki tukuru wajen magance waɗannan matsaloli da kuma samarwa ƴan Najeriya wutar lantarki yadda ya kamata.