Kungiyar Hausa ta jami'ar Bayero ta yi sabbin shugabanni.
An kafa ƙungiyar ne kamar sauran ƙungiyoyin jami'o'i domin haɓaka wannan sashe na Hausa aiwatar da tarukan da suka shafi ci gaban harshen Hausa da Hausa. Kuma ƙungiyar ta ɗalibai ce da za su rinƙa sanin darajar ilimin da suke koyo da kuma fito da kyawawan ayyukan sashen Hausa.
Ana yin zaɓe ne duk shekara, kenan duk zangon karatu ake samar da sabbin shugabanni, musamman saboda 'yan aji 4 za su tafi sai a maye gurbinsu.
Ana yin zabe ne ta hanyar kafa hukumar zaɓe, tare da bai wa ɗalibai damar yin zaɓe a junansu, amma da kulawar hukumar makarantar.
Ga jerin sunayen sabbin shugabannin:-
1.Kabiru Yusuf - Shugaba
2.Nasiru Abubakar - M/Shugaba
3.Hisnuddin Auwal Tahir - Magatakarda
4.Umar Nasir - M/Magatakarda
5.Isa Garba Usman - Jami’in Shirye-shirye
6.Khadija Yahaya Danjuma - Jami’ar Walwala
7.Zulaihat Safiyanu - Ma’aji
8.Zubairu Xahiru Turaki - Jami’in Hulxa Da Jama’a/PRO I
9.Mujahid Mansur - M/Jami’in Hulxa Da Jama’a/PRO II
10.Amina Sunusi Shamaki - Jami’ar Wayar Da Kai Da Wasanni
11.Hajara Shu’aibu Muhammad - Jami’ar KuÉ—i
Kuma ana zaɓen ne daga 'yan aji na 1 zuwa na 4, musamman an fi zaɓar 'yan aji na 4 a matsayin shugaba da mataimaki ko sakatare, ya danganta.
Akwai ƙudirori da yawa da muka da a gaba musamman da yake kungiyar ta yi barci, akwai tarin abubuwa da za mu aiwatar na dawo da martabarta. Kamar shirya tarukan wayar da kai ga sabbin ɗalibai, shirya tarukan sanin makamar karatu a zangon karatu da uwa uba shirya taron *Ranar Hausa* da ake yi a ƙungiyar. Sannan da shirya zabe idan muka kammala wannan zango namu.
A daya bangaren akwai gyaran ofis na kungiyar da samar da littattafai don dalibai da samar da motar zirga-zirga na kungiyar da sauransu. Muna fatan aiwatar da wadannan kudirori insha Allahu.
Tarihin kafuwar kungiyar Hausa abu ne mai faɗi, amma a taƙaice kamar yadda na faɗa an kafata ne saboda ɗalibai, kuma manyan malamai na wannan sashe sun taɓa zama shugabanninta ko membobi. Sannan sananniyar ƙungiya ce da take raya al'adun Hausawa da bayyana alfanun karantar wannan harshe mai albarka.
A karshe muna fatan shugabannin siyasa da masu hannu da shuni za su shigo su cicciɓi wannan kungiya domin kamar sun ƙara haɓaka harshen Hausa ne da kawo masa ci gaba.