Ƙungiyar matasan ƴan jarida reshen jihar Kano, wato Kano Youth Journalist Forum, ta yi kira ga majalisar dattawan ƙasar nan, da ta gaggauta janye dakatar da Sanata Abdul Ahmed Ningi, da ta yi har na tsawon watanni uku a baya-bayan nan, bisa tauye masa haƙƙi da ma na waɗanda yake wakilta a zauren majalisar dattawa.
Shugaban ƙungiyar matasan ƴan jaridar Musa Zangina Adam, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar, ya ce basa goyon bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi, duba da yadda yake ƙokarin kare muradun al'ummar Arewacin ƙasar nan, la'akari da yadda ya rinƙa ƙoƙari akan cushen da ya yi zargin an yi, a cikin kasafin kuɗin 2024.
A makon da ya gabata ne dai majalisar dattawan ta bakin shugaban ta Godswill Akpabio, ta bayyana dakatar da Sanata Abdul Ningi, daga ayyukan majalisar bisa zargin sa da zubar da kimar majalisar, inda a hirar sa da sashen Hausa na BBC, ya zargi majalisar da yin cushe a kasafin kudin ƙasa na 2024, lamarin da bayan amincewar mafi rinjayen ƴan majalisar aka dakatar da Ningi tsawon watanni uku.
“Muna kira da babbar murya ga masu ruwa da taki da su yi duba na tsakani domin ganin an janye dakatar da Sanata Abdul Ningi, ya ci gaba da aikinsa a zauren Majalisar dattawa domin ci gaba da wakiltar al'ummar sa; kuma muna Allah wa dai da dakatar da sanata Ningi, "in ji Zangina”.
Musa Zangina ya kuma ƙara da cewa, La'akari da cewa yanzu al'ummar da dakataccen sankaran Bauchi ta Tsakiya Sanata Abdul Ahmed Ningi, basu da wakili a majalisar dattawan kusan tsawon watanni uku, a dan haka akwai buƙatar a janye matakin dakatarwar ga Ningi, kasancewar akwai take hakki a cikin lamarin.