Hakan na zuwa ne a wani taron bita ta kara sannin makamar aiki da kungiyar NUJ ta hadawa ma'aikata gidan talabijin na ARTV,
Hajiya Hauwa Isah Ibrahim ta karbi shaidar ta hannun kwamishinan watsa labarai na Jahar Kano Baba Halilu Dantiye.
Baba Dantiye ya yabayawa Hajiya Hauwa Isah Ibrahim a bisa yadda take gudanar da aiki tukuru babu sanya.
Datake karbar shaidar Maigirma DMD Hajiya Hauwa Isah Ibrahim tayi godiya da wannan karramawar, kuma ta shawarci yan jaridu wajen jajircewa akan ayyukansu domin sauke nauyin da Allah ya dora musu.
Taron yasami halattar Kwamishinan watsa labarai na Jahar Kano, da maimakiyar shugaban gidan talabijin na Abubakar Rimi, da sauran ma'aikatan gidan dama tsofaffin ma'ikatan.