Kwamitin Samar da zaman lafiya na jihar kano (KPC),yayi Allah wadai da abun da wasu batagarin matasa sukeyi a unguwar Dorayi na yin fadan daba da sauran wasu manyan laifuka.
Wannan na kunshe ne a cikin wani sagon murya da shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiya na jihar Amb. Ibrahim Waiyya ya rabawa manaima labarai ta hannun mataimaki na Musamman kan kafafen yada labarai, Bashir A Bashir.
Kazalika Ambasada Ibrahim Waiyya ya bayyana cewa kwamitin zaman lafiya na Kano na yabawa rundunar yan sandan jihar kano Karkashin Jagorancin, CP Usaini Gumel duba da irin kokarin da sukayi na samar da tsaro cikin gaggauwa a yankin na Dorayi, tare da yadda aka samar da ofishin da zaiyi yakin da ayyukan daba a yankin da kewaye,harma da nasarar kama wasu daga cikin masu hannu da aikata wannan laifi.
Daga karshe Kwamitin zaman lafiya na jihar nan Kano Peace Committee yayi kira ga sauran alummar musamman na yankin Dorayi dasu cigaba da bawa Jami'an tsaro hadin kan da ya dace, musamman wajan bayar da bayanin sirri domin samun nasarar da ake bukata na yaki da fadan daba.