Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa, wani mai suna Alhaji Yusuf Adamu, ne, ta hannunsa lauyan H.I. Dederi, ya shigar da korafi ,ga mataimakakin sufeton Yan sandan Nigeria dake kula da shiya ta daya, AIG Umar Mohd Sanda, a ranar 18 ga watan Ogustan 2022, da cewar, wani Ramadan Inuwa, ya karbi kudin kasuwancin wayoyin salula har Naira miliyan arba’in, amma tunda ya Karba bai sake ganinsa ba.
A tattaunawar da Jaridar Idongari.ng, ta yi da mai magana da yawun rundunar Yan sandan Nigeria shiya ta daya (Zone 1 Kano ) CSP Bashir Muhammed, ya shaida cewa , binciken Yan sandan, ya gano an tura wa Amal Umar naira miliyan 13 cikin asusun bankin ta.
CSP Bashir, ya ce sun gaiyaci Amal Umar, domin ta amsa wasu tambayoyi, kuma bayan haka sun bayar da belin ta, sai dai ba su barta ta tafi da Wata mota, mai namba NSR 858JH, da ake zargin saurayin ya siya mata.
” Kudin da suke cikin Asusun banki na, na saurayi na ne”cewar Amal Umar amma naira miliyan takwas ne “.
Tun daga lokacin da aka bayar da belin Amal Umar, ne ta garzaya gaban Wata babbar kotun jahar Kano, don Hana Yan sanda ci gaba da gudanar da bincike akanta.
Inda kotun ta dakatar da jami’an Yan sandan kan Ci gaba da gudanar da bincike kan Amal Umar mazauniyar Tishama Hotoro Kano.
Wannan damar ce ta ba wa, yar wasan Hausar zuwa rundunar shiya ta dayan, don ta karbi motarta , har ta yi yunkurin bayar da cin hanci Naira dubu dari biyar (N500,000:00) ga jami’in dan sandan da yake bincike wato ASP Salisu Bujama.
Amal , ta bayar da Kafin alkalamin naira dubu dari biyu 250,000 da nufin za ta ciko ragowar , inda dan sandan ya Kama ta da hujjar da za ta sanya a gurfanar da ita a gaban kotu.
Kakakin rundunar Yan sandan shiya ta daya CSP Bashir Muhammed, ya ce wannan dalilin ne , ya sanya suka gurfanar da jarumar fina-finan Hausar , a gaban kotun majistiri dake unguwar gyadi-gyadi Kano , bisa zargin ta da yunkurin bayar da cin hanci ga jami’in dan Sanda Wanda yin hakan ya Saba da sashi na 118 na kudin Penel Code.
CSP Bashir Muhammed, ya ce , mataimakin sufeton Yan sandan Nigeria AIG Umar Mohd Sanda, ya gargadi Yan sandan shiyar su ci gaba da yakar cin hanci da rashawa, wanda shi ne zai sanya a yi wa, Wanda aka zalinta adalci , kamar yadda Babban sufeton Yan sandan Nigeria IGP Kayode Adeolu Abegketun, ya bayar da umarni.
A karshe ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike kan kudin da ake zargin sun yi batan dabo tsaninta da saurayin ta, don ba wa Kowa hakkinsa.