Al’ummar wadancan garuru dai sun jima suna fama da matsalar ruwa shekara da shekaru, wanda ta kai basa samun ruwan sha har sai sun yi tafiya sama da Kilomita biyu, hakan kuma yasa wasu da yawa daga cikin ya’yansu basa iya zuwa Makarantan.
Bayan samun koken nasu ne Sanatan Kano ta Arewa kuma mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta kasa Barau Jibrin Maliya ya bayar da umarni samarwa da jama’ar garuruwar rijiyoyin masu amfani da haske rana domin kawo karshe matsalar ga jama’ar garuruwar.
Wannan aikin samar da ruwan sha da sanata Barau Jibril ya samar zata taimaka matuka wajen magance matsalar ruwan