Matasan sun yi wa rumbun dirar mikiya ne da misalin karfe 7 na safe, inda suka yi wawushe buhunan masara da kuma na hatsi.
Mai magana da yawun Æ´ansandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatarwa da BBC faruwar lamarin, inda ta ce tuni suka tura jami'ansu zuwa yankin domin shawo kan lamarin.
Rahotanni sun bayyana cewa fasa rumbun abincin ya janyo cushewar hanyar Gwagwa-Karmo, wadda kuma ta dangana da anguwan Dei-Dei da kuma wani É“angare na Jabi.
Ƴan Najeriya da dama dai na ci gaba da kokawa kan matsin rayuwa da suke ciki biyo bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi.
Tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnatin ta zo da su, sun janyo hauhawar farashin kayan abinci wanda ba a taɓa gani ba a baya-bayan nan.