Yayin gabatar da bitar mai taken "SABUWAR HANYAR KASUWANCIA DUNIYA", Engr. Rabiu yaja hnkalin daliban kwalejin das u maida hankali wajen ganin sun koyi abunda malaman su ke iya kokari na ganin sun koya musu kuma saboda zai matukaramfanar dasu a rayuwa inda yayi misali da kansa cewa a baya kafin yanzu yana dalibi kamarsu ya maida hankalin wajen ganin ya koyi abunda aka koya masa wanda yayi sanadiyarzuwa matsayin daya tsinci kansa a yanzu, ka zaluka Engr. Rabiu ya kara da cewa zuwa makaranta a lokaci yana da matukar muhimmanci domin da yawan darusa muhimmai na wuce wanda basa zuwa makaranta a kan lokaci.
Haka shima Engr. Lawan Usman Isah shugaban kungiyar tsangayar injiniyoyi ta kasa reshen jihar kano ya gabatar da tashi mukalar inda a bangaren sa yaja hankalin dalibai dasu maida hankali wajen ganin sun kirkiro abubuwan da zasu dogara dasu wanda zai iya zama musu kari yayin da suka kammala karatun su.
itama sakatare janar ta wannan tsangaya Engr. Amina taja hankalin ɗaliban da a kullum su dunga tunanin dogaro da kansu don tallafawa kansu da kuma iyayen su a gida. Ta kuma bayyana cewa karatun su na zama injiniyoyi nan gaba yana daya daga cikin karatuttuka masu matuƙar muhimmanci a ƙasa saboda haka su maida hankali don ganin sunyi abunda ya dace.