Hisba Ta Yi Wa Malamin Da Ya Gyara Auren Saki Uku Bulala, Ta Kuma Zane Mata Da Mijin
Hukumar Hisba a Katsina ta yi wa wasu ma'aurata bulala da suka yi kome bayan sun rabu akan igiyar aure saki Uku, hukumar ta haÉ—a har da Malamin da ya maida masu Auren ta yi masu bulalar,
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a garin Ajiwa dake ƙaramar hukumar Batagarawa na Jahar Katsina, inda aka yi wa Yakubu Husamatu Ajiwa da Nafisa Adamu Ajiwa wanda ya saketa saki uku da kuma wani malami mai suna Malam Abdurrahaman Abdurra'uf wanda ya jagorancin mayar da Auren akan sadaki na Naira dubu hudu (4000).