Wajen daukar darassu na makarantar firamare ta gidan mai gari dake rafin dan malam dake yankin karamar hukumar ungogo na neman daukin mahukunta,
A wata ziyara da jaridar raihana takai wannan yanki ta iske wajen daukar darussa "azuzuwa" cikin wani hali, wanda daliban wannan makaranta ke daukar darussa a kasa.
Haka kuma mafiya yawan azuzuwan nabukatar neman daukin gwamnati sakamakon sumuntin ya farfashe, haka kuma wasu azuzuwan suna amfani da buhu ne dalibai nazama.
Wasu azuzuwan kuwa basu sami koda da damar buhun ba, iyayen daliban wannan makaranta sunbayyabawa jaridar raihana cewar a duk sanda yaransu sukaje makaranta to tabbas sai sunemo kudin omon wanki,
Sakamakon yaransu na karatu acikin turbaya, hakan yasa suka roki gwamnati data dubi Allah da Ma`aiki ta ceto yaransu daga wannan yanayi.
Ta sanya musu bencina da wadatattun kayan koyo da koyarwa.
Suma wasu malamai da suka nemi asakaya sunansu sunce lallai wannan makaranta na bukatar dauki daga mahukunta.