Umarnin shigo da kayan masarufi daga iyakokin kasar Najeriya shine abunda al'ummar Najeriya ke buƙata sama da komai a halin yanzu.
Amb. Ibrahim Waiya shugaban haɗakar ƙungiyoyi masu zaman kansu na arewacin najeriya ciki har da babban birnin tarayya ne ya bayyana hakan a wata takardar manema labarai da ya fitar ta hannun mai taimaka na musamman kan kafofin yada labarai Bashir A Bashir.
Amb. Waiya yace shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bada dama a shigo da kayan abinci domin shine hanya ɗaya tilo da al'ummar Najeriya zai samu sassauci a yanayin da ake ciki na halin yunwa da sauran sace-sace da ake fama dashi na dalibai a kasar nan.
Har yanzu shugabannin Najeriya suna amfani ne da shinkafar ƙasar waje a gidajen su amma sun hana talakan kasa samun ta waje sun ce sai dai ya noma yaci.