Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci rantsar da kwamishinoni guda hudu cikin ƙunshin Gwamnatinsa a wannan rana.
Taron rantsuwar ya gudana ne a Dakin taro na Africa House dake fadar Gidan gwamnatin Kano, inda Mustapha Rabi'u Kwankwaso ya zama sabon kwamishinan ma'aikatar matasa da wasanni, sai kuma Abduljabbar Garko a matsayin sabon kwamishinan ma'aikatar ƙasa da safayo.
Ragowar sun hada da Shehu Aliyu Yanmedi a matsayin sabon kwamishinan ma'aikatar ayyuka na musamman, sai kuma Adamu Aliyu Kibiya a matsayin kwamishinan ma'aikatar kasuwanci da masana'antu.
Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano, Jabir Ali Danabba, ya rawaito mana cewa, gwamnan ya kuma canjawa wasu kwamishinoni ma'aikatu, inda Abbas Sani Abbas ya koma ma'aikatar raya karkara sai kuma Amina HOD zuwa ma'aikatar jin ƙai.