Ba ga watan Shawwal ba a kasar Saudiyya, Kusan shi ne babban Labarin da ya karade jaridu da shafukan sada zumunta a Ranar Litinin a Najeriya.
Hakan ya biyo bayan yadda al’ummar musulmi suka Æ™agu wajen ganin watan Shawwal, wanda hakan ke nuna karshen watan azumi a bana.
To sai dai murna ta koma ciki, bayan da kasar Saudiyya ta tabbatar da cewa masu duban watan basu gan shi ba, kuma azumi ya tabbata 30 za ayi.
To sai dai a Najeriya a can jihar Sokoto an samu wani malami da ya ce shi an tabbatar masa da ganin wata a jamhuriyar Nijar, don haka sun kammala azumi shi da mabiyansa.
Haka kuwa aka yi, domin ranar Talata suka gudanar da sallar idi, kamar yadda a jamhuriyar Nijar suma suka gudanar da sallar su.
Yanzu haka dai ta tabbata gobe Laraba Sallah, biyo bayan cika watan Ramadan, kuma babu bukatar sai an sanar da ganin wata don ajiye azumin.
Da haka Jaridar Raihana ke taya al’ummar musulmi musamman masu bibiyar ta murnar sallah karama, da fatan kasancewa cikin bayin da suka rabauta a azumin da aka kammala a wannan mako.