Wata babbar kotun jihar Kano ta sanya ranar 17 ga Afrilu, 2024, domin gurfanar da tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa, da dansa, da wasu mutane biyar, bisa zargin karbar rashawa.
Za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume takwas da suka hada da zargin karbar cin hancin $413,000, da karkatar da kudaden da suka haura miliyan dubu.