Akwai Yuwuwar Saukar Farashin Kayan Abinci Warwas daga Litinin Mai zuwa a wasu Kasuwanni musamman Kasuwar Abinci ta Singer Dake Jihar Kano
Wani Dan kasuwa da ya Nemi mu sakaya Sunansa ya shaidawa wata kafar yaÉ—a labarai a nan Kano Cewa Tuni ya Umarci Dukkan Shagunansa da su Sauya Farashin Kayan daga Ranar Litinin Mai zuwa
Yace Matakin Saukakawa al'umma na rage Farashin Kayan Abinci yazo Daidai da kokarin da Sukeyi na Rage Farashin Domin baiwa al'umma Damar Sayen Kayan Abinci Cikin Sauki
Rahotanni Sun Bayyana Cewa Yanzu Haka Akwai Wasu kayayyaki da Farashin su ya Fara sauka, sakamakon Saukar Dalar Amuruka, da Kuma Kokawa da al'umma keyi na Rashin tausayi ga Yan Kasuwar.