Rashin bayyanar Ganduje a gaban kotun a yau ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin wadanda suka je sauraren karar, yayin da suke kokarin tantance ko rashin bayyanar Ganduje Rashin girmama kotu ne .
Sauran wadanda ba su halarci kotun ba sun hada da matarsa, Farfesa Hafsat Ganduje, danta, Umar Ganduje, da wasu mutane 5 da ake zargi .
Sai dai ba a bayyana dalilin da ya sa tsohon gwamnan wanda kuma shi ne shugaban jam’iyya mai mulki na kasa ya kasa bayyana a gaban kotu, amma wasu makusancinsa da ba a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa “Dr. Ganduje ba ya kasar.”
A ranar 9 ga Afrilu, 2023 babbar kotun jihar Kano ta bayar da sammaci ga shugaban jam’iyyar APC na kasa da ya gurfana a gaban kotu a ranar 17 ga watan Afrilu kan zargin almundahana na biliyoyin naira da aka tafka a lokacin da yake kan mulki.
Har zuwa lokacin hada wannan rahotan, ba a bayyana ko ya aike da wakilci kotun ko a’a ba .
Majiyar jaridar kadaura24 ta independent Post ta rawaito ana sa ran kotun za ta bayar da cikakken martani kan rashin halartar duk wanda ake tuhuma.