Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nada karin masu ba shi shawara na musamman da sauran shugabannin hukumomin gwamnati.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikewa Manema labarai
Wadanda Gwamnan ya amince da Nadin nasu sunhada da
(1). Farfesa Ibrahim Magaji Barde, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tattara kudaden shiga (IGR).
(2). Dr. Abdulhamid Danladi, mai ba da shawara na musamman kan harkokin yan kano Mazauna kasashen waje II
(3). Engr. Bello Muhammad Kiru, mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa.
(4). Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) an sake nada shi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni.
(5). Dr. Nura Jafar Shanono an dauke shi daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Daraktan hukumar (WRECA).
(6). Hon. Haka kuma Baba Abubakar Umar an dauke shi daga mai ba da shawara na musamman zuwa babban sakataren gudanarwa, na hukumar kula da karantu masu zaman kansu da na sa kai.
(7). Hon. Nasir Mansur Muhammad an nada shi Darakta Janar, Kanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs).
(8). Aminu Hamidu Bako Kofar Na’isa zai zama mataimakin Manajan Darakta (DMD), Hukumar Noma da Raya Karkara ta Kano (KNARDA).
(9). Engr. Mukhtar Yusuf, Mataimakin Manajin Darakta (DMD), hukumar WRECA.
Haka Kuma Sanarwar tace nade-naden sun fara aiki ne nan take.