Mai bai wa jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a a mazaɓar Ganduje ne Haladu Gwanjo ya sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar a wani taron manema labarai da aka yi a Kano ranar Litinin.
Gwanjo ya bayyana cewa matakin dakatar da Ganduje daga jam'iyyar ya faru ne saboda zargin da gwamnatin Kano take masa na aikata rashawa da wadaƙa da kuɗaɗe.
A cewarsa, mambobin jam'iyyar sun yanke shawarar dakatar da shugaban APC na ƙasa ne bayan ƙuri'ar yanke ƙauna da aka kaɗa a kan shi saboda gazawarsa wajen wanke sunansa daga tarin zarge-zargen da aka yi masa na rashawa da cin hanci.
Zarge-zargen dai sun haɗa da wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa wanda a ciki ake zargin sa da karɓar cin hanci daga ɗan kwangila.
Gwanjo ya bayyana cewa matakin ya fara aiki daga yau ɗin nan - 15 ga watan Afrilu