A wani mataki da ka iya girgiza yunkurin jihar Kano na yaki da cin hanci da rashawa, Kotun da’ar ma’aikata ta dakatar da Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Muhuyi Magaji.
An gurfanar da Magaji a gaban kuliya bisa manyan zarge-zarge, da suka hada da saba ka’idojin da’a ga jami’an gwamnati, da yin rikici da juna, cin zarafin ofishinsa, da bayar da bayanan karya kan bayyana kadarorinsa.
Ana kuma zarginsa da cin hanci da karbar kyaututtuka.
Kotun ta goyi bayan wanda ya shigar da karar, inda ta umurci Magaji da ya ajiye mukaminsa na Shugaban Hukumar.
Ba zai iya cika aikinsa a Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ba har sai an saurari tuhume-tuhumen da ake yi masa, sannan a yanke hukunci.
Wakilinmu Bashir A Bashir Tudun wada ya rawaito mana cewa kotun ta umurci gwamnan jihar Kano da sakataren gwamnatin jihar da su nada shugaban riko na hukumar domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar a wannan lokaci