Hajiya Yauwa Isah Ibrahim tarabawa mabukata tallafin kayan abinci 200, ta kuma rabawa marayu kayan sallah 100 domin gudanar da bikin sallah kamar kowanne da,
Datake bada tallafin Haj Hauwa Isah tace duba da yanayi da ake na matsananci yanayi yasa itama taga dacewar bada tallafin ga mabukata, ta kuma ce suma marayu yarane kamar kowa kuma yana da kyau a tallafa musu domin rage musu radadin rashin iyaye da suka rasa.
Haka zalika ta shawarci jama'a wajen gudanar da addu'oi na musamman musamman a lokacin da ake bankwana da watan Ramadan domin neman daukin Ubangiji acikin halin matsi da al'umma suke ciki, dama ninka ayyukan alkhairi domin ba lalle ne kowa yaga zagayowar shekara mai zuwa ba.