Zargin ya biyo Baya ne bayan an turo wasu magina Domin Gina maƙabartar da summary gina kamfani Na wani mutum a wajen, Inda daga bisani al'ummar unguwar dawakin dakata suka nuna damuwa Kan yadda suka ce ko tausayi babu anje ana gina kaburburan iyayen su ana neman mayar da gurin ma'aikata mallakin wani mutum dai Basu san wane ba.
Auwalu Nakowa guda ne cikin mazauna unguwar ta Dawakin Dakata Inda muka tattauna dashi dangane fa faruwar al'amarin ya Kuma bayyana mana cewa, sun wayi gari da ganin ana gina maƙabartar su Wanda hakan ya jefa su cikin takaici matukar, sannan sun nemi kin ba'asi ance music Na wani ne mai suna (Abba Rangaza) Dangidan maigarin Rangaza, Wanda Ko a baya-bayan nan anji Shi ana Shari'a da Mahaifinsa a gaban kotu Kan cefanar day wasu filayen da ba mallakin sa ba.
Mun nemi ji ta bakin maiunguwar ta Dawakin Dakata Har ma da Shi Wanda Ake zargi wato Abba Rangaza da Mahaifinsa maigarin Rangaza amma haƙan mu yaci tura.